Hira da Muhammad Baba Yahaya Babs na kamfanin Startimes na kasar Sin
2019-05-17 14:13:23 CRI
A kwanan baya, sashin Hausa na CRI ya samu bakuncin wani jarumi daga masana'antar shirya finai finai ta Noollywood daga Najeriya, kuma a halin yanzu ma'aikaci a kamfanin fasahar sadarwa ta zamani da watsa labarai ta tauraron dan adam na kasar Sin wato Startimes, Muhammad Baba Yahaya wanda aka fi sani da Babs. A wata hirar da wakilinmu Ahmad Inuwa Fagam ya yi da jarumi Babs, Babs ya bayyana irin gwagwarmayar da ya sha a fagen shirya fina finai da kuma irin nasarorin da ya cimma a masana'antar. Ga yadda hirar tasu ta kasance.