logo

HAUSA

Hira da Usman Adamu Ahmad malami a kwalejin ilmi ta Sa'adatu Rimi dake jihar Kanon Najeriya

2019-05-17 14:29:39 CRI



A cikin shirin Sin da Afirka na wannan mako, za ku ji wata hira da abokinyar aikinmu Fa'iza Muhammad Mustapha ta yi da Usman Adamu Ahmad, malami ne a kwalejin ilmi ta Sa'adatu Rimi daga jahar Kano a Najeriya, inda ya yi tsokaci game da irin manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a wannan zamani da muke ciki tun bayan da kasar ta aiwatar da manufarta ta yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, a cikin kalamansa ya bayyana wasu matakai daban daban wadanda kasar Sin ta dauka musamman ta fuskar raya aikin gona, da bunkasa masana'antu, da kyautata kirkire-kirkire a bangaren fasahohin zamani da dai sauransu. Hakazalika ya bayyana fatan alheri game da kyautatuwar danganataka tsakanin Sin da Najeriya har ma da nahiyar Afrika baki daya, bugu da kari, ya yi tsokaci da kuma bada shawarwari ga al'ummar Najeriya da jama'ar kasashen Afrika baki daya da su koyi halayyar Sinawa wajen sadaukar da kai da jajircewa da kuma sanya kishin kasa don kyautata yanayin zamantakewar rayuwar al'ummar kasashen Afrika baki daya.