logo

HAUSA

FIFA da hukumar wasan kwallon kafar kasar Sin na hadin gwiwar bunkasa kwallon kafar kasar Sin

2019-05-16 14:03:53 CRI

Hukumar kwallon kafar duniya FIFA, da hukumar wasan kwallon kafar kasar Sin sun amince da gudanar da hadin gwiwa, domin bunkasa kwallon kafar kasar Sin. Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino, tare da shugaban hukumar kwallon kafar Sin CFA Du Zhaocai, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya a helkwatar FIFA a ranar Larabar makon jiya. Da yake tsokaci game da hakan, Mr. Infantino ya ce burin FIFA shine, tabbatar da ci gaban kwallon kafa a kasa mafi yawan al'umma mai kuma tasowa a yanzu. Ya ce kwallon kafar Sin ta dade tana gwagwarmayar samun bunkasa, kuma ko shakka babu wannan yarjejeniya da aka kulla tare da FIFA za ta samar da tsarin tallafawa ci gaban da ake fata. Rahotanni sun bayyana cewa, hadin gwiwar FIFA da CFA na kunshe da tsarin kyautata gudanarwar kwallon kafa, da fannin samar da horo a fannin raya wasan. Bisa wannan buri, an amince da daukar muhimman matakai guda 5, wadanda suka hada da kyautata tsarin gudanarwar hukumar CFA, da gina tsarin samar da kwarewa a dukkanin fannonin wasan, da fannin alkalancin wasa, da bunkasa kwarewa a fannin tsara wasanni da gasanni. An dai sanya hannu kan yarjejeniyar ne bayan taron yini guda tsakanin jami'an FIFA da na CFA, inda sassan biyu suka tattauna game da sassan samar da kwarewa, da fannin yayata wasan, da na hulda da jama'a, da na jagoranci da na kula da jami'ai. A nasa tsokaci Du Zhaocai, ya ce a matsayin ta na kasa da ke fatan samar da karin ci gaba a fannin kwallon kafa, Sin a shirye take ta ba da gudummawa, wajen hade kungiyoyin ta na kwallon kafa da na sauran kungiyoyin kasa da kasa. Jami'in na hukumar CFA ya kara da cewa, hukumar sa na da fatan ci gaba da mara baya ga hukumar FIFA, domin ci gaban kwallon kafar Sin, wanda hakan mataki ne na bunkasa kwallon kafar duniya baki daya.

An zabi Du Zhaocai ba da dadewa ba, domin zama dan majalissar gudanarwar FIFA na tsawon shekaru 4, wato ya zuwa shekarar 2023.(Saminu Alhassan)