logo

HAUSA

Dani Alves yana burin taka leda a gasar kofin duniya ta 2022 a lokacin da zai shekaru 39 a duniya

2019-05-16 13:58:43 CRI

Dan wasan kungiyar Paris Saint-Germain kana dan wasan gaban Brazil Dani Alves ya bayyana sha'awarsa na daga matsayin wasan a matakin kasa da kasa a kasar cin kofin duniya ta shekarar 2022, wadda za'a buga kasa da watanni 6 gabanin ya cika shekaru 40 a duniya. Alves wanda ya rasa wasan kofin duniya na bara a kasar Rasha bayan da ya samu rauni a tafin kafarsa na dama makonni kadan kafin a fara gasar. Dan wasan mai shekaru 35 da haihuwa yace tunaninsa shine babbar kadararsa ba wai gangar jikinsa ba, zai kasance daga cikin masu halartar horo na musamman na kasar Brazil wanda za'a yi a Qatar. "Burin da nake dashi shine zuwa wancan waje," Alves ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Folha de S.Paulo ta kasar Brazil ta wallafa. "Na san cewa har yanzu al'amari ne mai wahalar gaske samun damar zuwa wancan wajen amma a rayuwa ya kamata ka dinga hararo manufofinka kuma ka dinga shirye shiryen yadda zaka cimmasu." Tsohon dan wasan Barcelona, Juventus kana mai tsaron bayan kungiayr Sevilla ya kara da cewa: "Ina tunanin a wasan kwallon kafan wannan zamani basira itace komai, duk da yanayi na lafiya. Akwai mutane da dama da suke gudu da yawa amma tunaninsu kadan ne. Wadan nan da suke yin tunani suna iya kara samun wata karin dama. Nasan cewa idan har ka kai wannan shekaru mutane suna tunanin baka da wani abu da zaka iya bayarwa. Amma shirye shirye basu tsaya a iya yanayi na zahirin jiki ba. Dole suna shafar batu na tunani." Alves, wanda ya dawo kungiyar wasan Paris Saint-Germain a watan Nuwamba, yana ganin cewa Brazil zata iya dagawa zuwa matsayi fiye da matakin kusa da kusan karshe a gasar Rasha – inda suka tashi da ci 2-1 da Belgium.. "Babu tantama babban burin da aka sanya gaba shine Brazil ta yi nasarar daukar kofin a gasar cin kofin duniya. Banbancin dake tsakanin kofin duniya dana [UEFA] Champions League shine kofin duniya yana sanya kasa cikin farin ciki. Amma na Champions League wani bangare ne na masu sha'wara wasannin ne kawai. Alves ya bayyana irin kyakkyawar abokantaka tsakanin kulub din Brazil da tawagar kungiyar wansan Paris Saint-Germain ta Neymar, inda ya buga a Barcelona daga shekarar 2013 zuwa 2017. A cewar Alves, Neymar ya fuskanci sukar ra'ayi saboda zumudinsa a gasar kofin duniya ta 2018.

"Babu inda zai yi da ransa, " inji Alves. "Shi dan adam ne, ba inji bane. Neymar tamkar da ne a waje na...Na san abinda yake cikin kwakwalwarsa. Amma Neymar yana da matukar basira. Yana da wani hali dake sa mutane jin haushi : Shi attajiri ne, shaharar kuma kyakkyawa.(Ahmad Fagam)