logo

HAUSA

Tennis: Wani gwajin kimiyya ya fara samar da damar hasashen irin salon da dan wasa zai buga kafin wasan sa

2019-05-16 14:01:11 CRI

Masana ilimin kimiyya sun kirkiri wani tsarin gwaji, dake amfani da yadda dan wasan Tennis ya biga wasa a baya, domin hasashen irin yanda zai buga wasannin sa na gaba. Masu bincike daga jami'ar fasaha ta Queensland dake Australia, sun yi amfani da bayanan wasu wasanni na gasar Australia Open, na 'yan wasa irin su Novak Djokovic, Rafael Nadal, da Roger Federer, tun na shekarun 2012, domin samar da hasashe na irin kwallayen da za su buga a wasannin karshe, na manyan wasannin su na baya bayan nan. Dr. Simon Denman ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Talata cewa, domin gudanar da wannan bincike, an yi amfani da bayani daga manhajar "Hawk-eye" a gasar Tennis ta Australia, irin bayanan da ake amfani da su, wajen baiwa alkalan gasar tallafin gano ko kwallo tana cikin layukan filin wasa ko ta fita. Duk da cewa sakamakon da gwajin ya samar ba ya bada hasashe dari bisa dari, amma Dr. Denman ya ce, ya ba da kyakkyawan bayani game da salon 'yan wasa. Denman ya kara da cewa, akwai wasu kwallaye da suka kaucewa hasashen, akwai kuma wadanda suka fada daidai da yadda aka yi hasashen su. Ya ce gwajin ya kuma samar da dama ga masu bincike, ta gane irin tsarin dokokin wasan, da wuraren da ya dace kwallon Tennis ta nufa, da kuma irin gyare gyaren da ya dace a aiwatar yayin da dan wasa ke buga wasan. Dr. Denman ya kuma ce ba duka 'yan wasa ne ake iya hasashen yanayin wasan su daidai da na saura ba. Alal misali a cewar sa, Federer na daga cikin mafiya wahalar hasashe saboda kwarewar sa, kuma hakan ya sanya bisa gwajin da aka yi, ya fi sauran 'yan wasa haifar da kuskure bisa alkaluman hasashen. Da yake karin haske game da wannan bincike, masanin ya ce abun takaici ne ganin cewa gwajin, ba zai iya ba da damar hasashe kan daukacin wasannin da aka buga yayin manyan gasannin da suka gabata ba.

Amma duk da haka, akwai dama ta hade sakamakon wannan gwaji da sauran dabaru, na kwaikwayar wasannin da aka buga da na'ura, a kuma yi hasashen wanda zai lashe wasa na gaba, duk da ba a kai ga yin hakan ba a yanzu. (Saminu Alhassan)