logo

HAUSA

Lippi yana gaf da komawa kasar Sin a matsayin mai horas da 'yan wasan babar kungiyar wasan kasar

2019-05-16 14:03:01 CRI

Kociyan kasar Italiya Marcello Lippi yana dab da fara aikinsa a wa'adi na biyu a matsayin kociyan babbar kungiyar wasan kasar Sin, wata majiya ce ta shedawa kamfanin dillancin labaran Xinhua. Majiyar tace, an kusan cimma yarjejeniya kan kwantiragin shekaru 4 kana kasar Sin a shirye take ta tantance Lippi don shiga gasar kofin duniya na shekarar 2022. "Lippi ya isa birnin Guangzhou a ranar Litinin kuma ya tattauna da jami'an kasar Sin," wata majiya dake da kusanci da Lippi ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua. "An gudanar da yarjejeniyar cikin nasara kuma dukkan bangarorin biyu sun kusan cimma matsaya duk da cewa ba'a bayar da cikakken bayani ba," inji majiyar. Dan wasan babbar kungiyar wasan kasar Sin wato China national futsal, Guan Zhichao, ya wallafa hotonsa a shafinsa na sada zumunta tare da mutumin mai shekaru 71 a duniya a sashen tashin jiragen sama na filin jirgin saman kasa da kasa na Guangzhou Baiyun airport. Lippi daga nan ya tashi zuwa kasar Italiya bayan cimma matsaya. "Ni da iyalina mun tashi daga Guangzhou domin zuwa hutu, wannan abin mamaki ne gareni dana hadu dashi a filin jirgin saman," inji Guan. "Lippi yana cikin yanayi mai kyau kuma yayi matukar farin ciki da yin hoto tare da ni da dana," injishi. Lippi ya fara aiki da babbar kungiyar wasa ta kasar Sin ne tun a watan Nuwambar shekarar 2016 kuma ya kammala a watan Janairun wannan shekarar bayan da bangarensa ya yi nasara da ci 3-0 a wasan da suka buga da Iran a wasan kusa da na kusan karshe na cin kofin Asiya. Dan kasar ta Italiya ya jagoranci kungiyar wasan ta kasar Sin inda suka yi nasara a wasanni 10 sannan suka tashi canjaras a wasanni 9 a cikin wasanni 30 da suka buga. Wani dan kasar ta Italiya Fabio Cannavaro, ya fice daga babbar kungiyar wasan kasar Sin a ranar Lahadi. Kociyan kungiyar wasan Guangzhou Evergrande ya karbi kungiyar wasan ta kasar Sin a watan jiya kuma ta rasa wasanni 2 a wasan da suka buga da Thailand da Uzbekistan a wasan cin kofin kasar Sin. Kawunan 'yan kungiyar wasan kasar Sin ya rabu game da yiwuwar komawar Lippi. Wasu sun yi amanna cewa dan kasar ta Italiya zai iya kaiwa kungiyar wasan zuwa matakin neman kofan duniya, amma wasu na ganin cewa 'yan kungiyar wasan kwallon kafan ta kasar Sin sun yanke mummunar shawara. "Lippi fitaccen kociya ne na duniya wanda ke da dunbun kwarewa a kungiyar wasan kwallon kafan ta kasar Sin, ya sake dawowa ne saboda yayi amanna cewa zai iya taimakawa kungiyar wasan ta kasar Sin cimma burinsu a gasar cin kofin duniya, lokaci ne kadai zai tabbatar da hakan," Wani mai sha'awar wasanni a kasar Sin ne ya wallafa wannan a shafinsa na sada zumunta na Weibo.

"Kungiyar wasan kwallon kafan kasar Sin sun sake bin mummunar hanya, mun kashe makudan kudade wajen daukar hayar kociyoyi masu tsada da 'yan wasa daga kasashen waje. Yaya idan da ace mun zuba wadannan kudaden wajen kafa cibiyar horas da matasan 'yan wasa? Da yanzu mun samu nasarar kaiwa ga matakin shiga gasar cin kofin duniya tun da jimawa," inji wani mai sha'awar harkar wasannin.(Ahmad Fagam)