logo

HAUSA

Wasannin lokacin sanyi dake samun karbuwa a kasar Sin

2019-05-16 14:01:50 CRI

Wasannin lokacin sanyi dake samun karbuwa a kasar Sin

A nan kasar ta Sin, an fara shiga wasannin kankara da wuri, ganin yadda kasar take da makeken yankin da ya kasance wurin da lokacin sanyinsa yana da tsayi. A da can, Sinawa sun taba yin amfani da wasannin kankara a matsayin wata dabarar atisayen sojoji, domin yakin da aka yi a arewacin kasar na bukatar sojoji su koyi fasahar yin amfani da takalmar wasan kankara. Domin biyan wannan bukata, sarkin kasar ya taba shirya wasu gasannin wasan kankara a shekaru fiye da 100 da suka wuce. Sa'an nan zuwa yanzu, wasanni masu alaka da kankara na kara samun karbuwa a kasar Sin, ganin yadda kasar take shirin karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin sanyi da za ta gudana a shekarar 2022. (Bello Wang)