IAAF ta amincewa kungiyoyi wasa 42 daga Rasha su taka leda a wasannin kasa da kasa
2019-05-16 14:00:18 CRI
Hukumar shirya wasannin motsa jiki ta kasa da kasa (IAAF) ta lamincewa kungiyoyin wasanni 42 daga kasar Rasha su halarci wasannin kasa da kasa, hukumar wasannin ce ta sanar da hakan. Hukumar tantancewa ta IAAF ta amince da bukatar kungiyoyin wasannin 42 wadanda suka cika ka'ida dasu shiga kasar wasannin motsa jikin na kasa da kasa wanda za'a gudanar a 2019 karkashin dokar wasanni ta 22.1A(b) yayin da ake cigaba da dakatar da hukumar shirya wasannin kasar Rashar, inji hukumar ta IAAF ta sanar da hakan a taron manema labarai. IAAF ta dakatar da kasar Rasha daga halartar wasanni ne tun a watan Nuwambar shekarar 2015 bayan zargin wasu daga cikin 'yan wasanta da yin amfani da magunguna dake bugarwa.
Daga cikin kungiyoyin wasannin Rasha da aka wanke tare da basu damar shiga wasannin akwai 'yar wasan tsalle wacce ta taba lashe gasar duniya har sau biyu Maria Lasitskene, da wacce ta samu nasara a gudun mita 110 Sergey Shubenkov da European pole vault silver medalist Timur Morgunov.(Ahmad Fagam)