logo

HAUSA

Kungiyar wasan kwallon Kenya Gor Mahia ta shiga "rukunin mutuwa" a gasar cin kofin Afrika

2019-05-16 14:01:34 CRI

Kungiyar wasan kwallon kafan kasar Kenyan Gor Mahia suna bukatar zage damtse mutukar suna son yin galaba a gasar cin kofin kasashen Afrika CAF saboda rukunin da kasar ke ciki a halin yanzu. Hukumar shirya gasar cin kofin kasashen Afrika (CAF) ta sanar cewa dole ne Kenyan ta sa kaimi domin karawa da kungiyar data dauki kofin na Afrika har sau biyar wato Zamalek ta kasar Masar a rukunin B. Sauran kungiyoyin da suke rukunin na B sun hada da kungiyar wasan Petro Atletico ta Angola data Algeria NA Hussein Dey. " A koda yaushe ba abune mai sauki ba buga wasa a wannan mataki. Amma mu kungiyar wasan Gor Mahia zamu yiwa kasar Kenya wasa mai kyau kuma 'yan wasa na suna da kwarewar fitar da kasar kunya. Sun sani dole ne zamu yi nasara," inji shugaban kociyan horas da kungiyar ta Gor Mahia Hassan Oktay. Kungiyar tana buga wasanni a cikin gida da kuma ketare Wadanda suka samu nasara a gasar zasu kara da wadanda suka samu nasara a gasar CAF Champions League domin samun damar taka leda a gasar kofin duniya ta FIFA. Holders Raja Casablanca sun tashi kunnen doki da ta Morroco RS Berkane da Hassania Agadir a rukunin A, da Congolese champions AS Otoho a wasan kusa da kusan karshe. Sakamakon yayi kama da irin sakamakon da aka samu a gasar da aka buga na shekarar 2012, inda Al Merreikh, da Al Hilal da Ahly Shendi ta Sudan suka tashi kunnen doki a rukuni daya. Yayin da rukunin A suke da kungiyoyi wasa 3 daga kasa guda, lamarin yayi kama da na rukunin B da rukunin C, wanda duka aka samu kungiyoyin wasa biyu-biyu daga kasa guda. Tunisian duo Etoile du Sahel da CS Sfaxien suna rukunin B tare da Enugu Rangers daga Najeriya da kuma surprise package Salitas ta kasar Burkina Faso. A rukunin C, Zambia tana kulob biyu - Nkana da Zesco, da Asante Kotoko ta Ghana sai Hilal ta Sudan.

Kotoko da Hilal suna da dadadden burin samun nasara, bayan da suka hadu a rukuni daya a gasar farko ta cin kofin CAF Confederation a shekarar 2004.(Ahmad Fagam)