logo

HAUSA

Wasan "Jianzi" na kasar Sin

2019-05-16 13:59:59 CRI


Wasan "Jianzi" na kasar Sin

Ta yaya ake wasa da "Jianzi"?

Fasahar wasan Jianzi ta shafi wasu motsin da za a yi don dinga buga Jianzi din sama, da hana shi sauka kasa. Za a iya yin amfani da duk wani bangaren jiki, ban da hannu, wajen buga Jianzi sama. Sa'an nan, bai kamata a bar Jianzi din ya tsaya kan wani bangaren jikin mutum ba. Wato, ya kamata a dinga daga shi sama. Wannan ya yi kamar dabarar da a kan dauka wajen kyautata fasahar buga kwallon kafa. A nan kasar Sin, an fi ganin wadanda suke wasan Jianzi a cikin makarantu. A lokacin darassin motsa jiki, kuma lokacin hutu tsakanin darussa, a kan ga yadda dalibai suka tsaya a filin wasa, su kafa wani jeri mai sifar da'ira. Sa'an nan daya daga cikinsu zai fara buga Jianzi zuwa sama, daga bisani wanda ke dab da shi zai karbi Jianzi din da kafa, shi kuma ya sake buga Jianzi din sama. Ta haka, ana ta buga Jianzi din zuwa sama a kai a kai, kuma ana mika shi da karbar shi tsakanin daliban. Manufar wasan ita ce, ko wane mutum zai buga Jianzi din karo guda, sa'an nan zai bar wani mutum na daban ya buga, kana za su yi kokarin hana ganin Jianzi din ya sauka kasa. Wannan shi ne dabarar da aka fi dauka wajen wasa da Jianzi a nan kasar Sin. Wani lokaci ma, idan wasu sun kware sosai a fannin buga Jianzi, za su iya gwada wani salon wasa, inda wani mutum zai dinga buga Jianzi da fasahohi daban daban, kamar ya yi tsalle tare da buga Jianzi da kafa, ko kuma ya daga kafarsa zuwa kusa da kansa don karbar Jianzi da ya sauka. Wasu kuma har suna iya tsalle da juya jikinsu a sama, haka kuma suna buga Jianzi din da kafa yayin da suke sama. Duk wadannan motsi an tsara su ne don kara wuyar sarrafa Jianzi, gami da samar da karin nishadi ga wadanda suka mallaki wadannan fasahohi.  

gasani masu alaka da "Jianzi"

Siffar "Jianzi" ta yi kama da kwallon "badminton", don haka ana iya gudanar da gasa ta "Jianzi" kamar yadda ake gudanar da gasanni na "badminton". Hakika filin wasan da ake yin gasar "Jianzi" ya hada da filin wasan "badminton". Sai dai ba a yarda da yin amfani da wata na'ura wajen buga Jianzi din, illa dai sassan jikin mutum, ban da hannu. Domin idan an yarda da yin amfani da hannu wajen yin wasan, zai zama matukar mai sauki, da kuma rashin kayatarwa. Kamar yadda ake gasar badminton, yayin da ake yin gasar "Jianzi", a kan raba 'yan wasa zuwa bangarori 2. Sa'an nan a duk wani bangare, akwai 'yan wasa su 3. Ragar dake tsakiyar filin wasa tsayinta shi ne centimita 90, wato bai kai mita daya ba. Wannan tsayi na baiwa 'yan wasa damar daga kafafuwansu zuwa sama don buga Jianzi din da karfi sosai, da nufin sanya Jianzi din ya sauka a kasan bangaren abokan karawarsu cikin sauri. Wannan fasaha ta sa yanayin wasan ya zama wani mai nishadi da burgewa. Ana shirya manyan gasannin wasan Jianzi a nan kasar Sin a kai a kai, musamman ma a fadar mulkin kasar, Beijing. Yanzu haka, a kan samu kungiyoyin kasashen waje, da suke zuwa kasar Sin don halartar gasanni, sakamakon yaduwar wasan Jianzi a kasashe daban daban. Wasu kamfanonin kasar Sin su kan ba da tallafi ga irin wannan gasanni, don an yi hayar wuraren gudanar da gasa, da samar da kyautar kudi da za a baiwa wadanda suka ci nasara a gasannin, ta yadda kamfanonin su ma suke samar da gudunmowa, ga kokarin yayyata wasan Jianzi na gargajiya a wannan zamanin da muke ciki.

sauran wasanni masu alaka da "Jianzi"

Saboda wasan Jianzi yana da dogon tarihi a nan kasar Sin, don haka Sinawa sun riga sun yada wannan wasa zuwa kusurwoyin duniya. Yanzu a kasashe daban daban, ana iya ganin wasan Jianzi, ko kuma wani wasan da ya yi kama da Jianzi, wanda aka nada masa wani suna na daban. Ga misali, a kasar Amurka, ana kiran wasan Jianzi da sunan "Chinese hacky sack" ko kuma "kikbo", sa'an nan a kasar Japan akwai "Kebane", wanda shi ma iri daya ne da wasan kasar Sin na "Jianzi". A kasar Birtaniya ana kiran wasan da sunan "featherdisk", yayin da a kasar Faransa ake kiransa "Pili".

Cikin sauran wasanni wadanda suka yi kama da Jianzi na kasar Sin, wanda ya fi farin jini shi ne "hacky sack", wato wasan buga wani karamin buhu, wanda yake da rairayi a ciki. Wannan wasa, idan an kwatanta shi da wasan Jianzi, za a ga cewa, tun da buhu yana da taushi ne, kuma bangarensa da zai taba kafar mutum ya fi na Jianzi girma, don haka wasan buhun zai fi wasan Jianzi sauki. Saboda haka yanzu haka wasan buhun nan na Hacky-sack ya fi samun karbuwa a kasashen dake nahiyoyin Turai da Amurka. Yayin da ake kokarin raya fasahohi na wasan Hacky-sack, an taba aron fasahohi masu sarkakiya na wasan Jianzi na kasar Sin. Daga bisani, saboda ci gaban wasan Hacky-sack, shi ma ya samar da dimbin fasahohi masu inganci, wadanda wasan Jianzi na kasar Sin shi ma ya koya. Wannan ma ya kasance wani bangare na cudanyar al'adu dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashe daban daban, kuma makasudin cudanyar shi ne nishadantarwa da kyatarwa. (Saminu Alhassan / Bello Wang)