logo

HAUSA

An bude bikin baje kolin lambunan shakatawa na duniya na Beijing

2019-05-09 09:14:59 CRI

Ranar Litinin 29 ga watan Afrilu da safe ne, aka shirya gagarumin bikin baje kolin lambunan shakatawa na duniya na Beijing, matakin dake nuna cewa, an bude gagarumin bikin da za a shafe kwanaki 162 ana yi ga masu yawon shakatawa na Sin da na kasashen ketare.

A yankin nune-nunen, an yi nune-nune kide-kide na zamani da wasu wasannin gargajiyar Sin, ciki har da wasan damisa da na dragon. A yankin wasu kasashe kuwa, an nuna raye-raye masu salon musamman irin na Brazil, Rasha, Faransa, Afirka, Turai, Scotland da kuma Hawaii da dai sauransu

Baki kimanin 900 ne suka halarci bikin kaddamarwa, ciki har da shugabanni da wakilai daga kasashe 11 da jami'an kungiyoyin duniya da abin ya shafa da sassan da za su baje kolin lambunansu da masu masana'antu da 'yan kasuwa da kwararru a fannin lambunan shakatawa da sauransu. Kafin bikin, shugaba Xi Jinping ya zagaya da shugabanni mahalarta bikin rumfar kasar Sin.

Girman filin ya kai mura'abba'in eka 503, ana kuma saran mutane miliyan 16 ne, za su kai ziyara. Ana kuma daukar bikin nune-nune a matsayin mafi girma a duniya. Taken bikin shi ne, gina kyakkyawan muhalli da dan-Adam da muhalli za su kasance tare.

A yayin bikin baje kolin, za a nuna manyan fashohin zamani da nasarorin da aka cimma a fannin lambuna daga sassan duniya daban-daban da ma irin ci gaban da kasar Sin ta samu wajen raya lambuna, kamar furanni da kayan marmari da ganyaye da tsirran magunguna da ganyayen shayi gami da wayewar kai a fannin muhallin halittu. A ranar 7 ga watan Oktoban wannan shekara ne, za a kammala bikin. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)