logo

HAUSA

Garin Wuzhen na lardin Zhejiang ya kasance abin koyi wajen gyaran fuska da bude kofa

2019-05-07 07:04:47 CRI

Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkanmu da sake kasancewa a cikin sabon shirinmu na "Allah daya gari bamban", shirin dake zuwa muku kai tsaye daga nan sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin tare da ni Jamila, to a yau zamu yi muku bayani kan garin Wuzhen. Garin Wuzhen yana karkashin jagorancin Tongxiang na lardin Zhejiang dake kudu maso gabashin kasar Sin, yana da tarihin wayewar kai mai tsawon shekaru sama da dubu 7, yanzu ba ma kawai ya shahara wajen yawon shakatawa bisa halayyar musamman tasa bane, har ma ya nuna rinjaye wajen ci gaban kimiyya da fasahar intanet a fadin duniya. A cikin shekaru 40 da suka gabata, wato tun bayan da gwamnatin kasar Sin ta fara aiwatar da manufar gyaran fuska a gida da bude kofa ga ketare, garin nan na Wuzhen ya yi kokari matuka domin samun ci gaba ta hanyar raya tattalin arzikin yawon shakatawa da sana'o'in dake da nasaba da intanet, har ya kasance abin koyi wajen gyaran fuska da bude kofa a fadin kasar ta Sin. Garin ya yi kusa ne da wasu birane wadanda suka fi saurin ci gaban tattalin arziki a kasar ta Sin, kamar su Hangzhou, hedkwatar lardin Zhejiang, da Suzhou, shahararren birnin yawon shakatawa na lardin Jiangsu, da kuma birnin Shanghai, a cikin garin, ko ina ana iya ganin koguna daban daban dake hadewa da juna, bisa sharadin hallitu mai inganci, garin Wuzhen ya samu ci gaba cikin sauri, ya zuwa karshen shekarar 2017, adadin GDP nasa ya kai kudin Sin yuan biliyan 6, kana adadin cinikayyar waje na garin ya kai yuan biliyan 3, har a karo na farko ne adadin masu yawon shakatawan da suka zo garin domin bude ido ya zarta miliyan 10. Darektan kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na garin Wuzhen Jiang Wei yana ganin cewa, dalilin da ya sa garinsa ya samu ci gaba cikin saurin haka shi ne domin manufar gyaran fuska a gida da bude kofa ga ketare da ake aiwatarwa a kasar ta Sin, saboda kirkire-kirkiren da ake yi, sai dai garin Wuzhen ya samu ci gaba ta hanyar raya tattalin arzikin yawon shakatawa, yana mai cewa, "A shekarar 1999, gwamnatin birnin Tongxiang ta tsai da kuduri cewa, zata kafa wani kwamiti domin kare albarkatun yawon shakatawa da raya aikin yawon shakatawa a Wuzhen, saboda garin yana mallakar dogon tarihin al'adu, daga wancan lokaci, gwamnatin birnin Tongxiang ta mayar da Wuzhen a matsayin tsohon garin yawon shakatawa." Idan ka shiga garin Wuzhen, zaka kalli doguwar hanyar da aka gina da manyan duwatsu, da shagon sayar da waina, da shagon samar da giya, zaka ji lokaci yana gudana cikin jin dadi, ko ina ni'imtattun wurare ne, amma kafin shekaru sama da goma, ba haka abin yake ba. Mataimakin darektan zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar birnin Tongxiang wanda ya taba shiga aikin raya garin Wuzhen Zhang Jianlin ya gaya mana cewa, kafin a fara kafa kwamitin kare albarkatun yawon shakatawa da raya aikin yawon shakatawa a Wuzhen, garin nan shi ma ya gamu da matsaloli daban daban kamar su koma bayan tattalin arziki da lalacewar tsoffin gine-gine da hanyoyi, ya ce: "A wancan lokaci, babu mutane da yawa a Wuzhen, gidajen kwana sun lalace, da dare kuwa babu hasken fitila a kan hanya, sai tsoffafi da yara ne kawai a garin, hanya bata da fadi ko kadan, har mota ba zata iya shiga ba, amma yanzu yanayin ya sauya." Bisa zurfafuwar gyaran fuska da bude kofa, ana kara maida hankali kan sana'o'in dake da nasaba da intanet yayin da ake kokarin raya tattalin arizkin yawon shakatawa a garin Wuzhen, musamman ma tun daga shekarar 2014 wato tun bayan da aka fara shirya babban taron intanet na kasashen duniya a Wuzhen, garin ya samu sabon ci gaba. A shekarar 2014, an shirya babban taron intanet na kasashen duniya karo na farko a garin Wuzhen, a wancan lokaci, gaba daya adadin kamfanonin dake gudanar da harkokin dake da nasaba da intanet ko tattalin arziki na zamani ya kai 12 ne kawai, amma yanzu sun riga sun kai sama da 500. Leo Caillard, masanin fasaha na kasar Faransa wanda ya taba shiga babban taron intanet na kasashen duniya karo na 5 a farkon watan Nuwamban shekarar 2018 da aka shirya a Wuzhen, yana ganin cewa, daga ci gaban intanet na Wuzhen, ana iya gano ci gaban intanet na kasar Sin, ya ce: "A Wuzhen, naji ana iya hada gargajiya da zamani, wato ba ma kawai a martaba gargajiya ba, har ma ana kokarin raya sabuwar fasahar zamani, gwamnatin Wuzhen tana maraba da zuwan masu gudanar da aikin intanet ba tare da rufa rufa ba, domin su tattauna batutuwan da suke jawo hankalinsu a nan, ina saran cewa, kasashen Sin da Faransa zasu kara gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin fasahar zamani a nan gaba." Yanzu a bakin kofar shiga lambun shan iska na Wuzhen, ana amfani da na'urar tantance hoton fuska, ana iya kammala aikin tantance hoton fuska cikin dakika 0.6, idan kana son hawa kan keken da ake samarwa ko kana son shiga jirgin ruwan kan kogi cikin lambun shan iska, to kana iya kiran keken ko jirgin da wayar salula kai tsaye, kana, idan kana son shiga otel, an riga an samar maka na'urar yin rajista, bayan na'urar ta tantance hoton fuskarka, zaka iya shiga dakin da ka yi oda lami lafiya. Ban da haka, an kafa shago maras ma'aikata a ciki, kuma an samar da na'urar mutum mutumi mai sarrafa kanta irin ta tsabtar bolar da aka jefa, da jigilar kayayyaki zuwa ga masu bukata daga wuri mai nisa, duk wadannan sauye-sauyen da aka samu a Wuzhen sun nunawa al'ummmomin kasashen duniya cewa, garin Wuzhen yana cike da fasahohin zamani. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, bisa bunkasuwar tattalin arzikin garin Wuzhen, haka kuma bisa tasirin da babban taron intanet na kasashen duniya ya haifar, wasu biranen dake kusa da garin su ma sun samu damammakin ci gaba, misali kamfanin samar da tufafi na Hengmei na birnin Jiaxing na lardin Zhejiang yana sauka ne a wurin dake kusa da Wuzhen, kamfanin yana nazarin fasahar zane tufafi yana samar da tufafi kuma yana sayar da tufafi ga kasashen waje, yanzu kamfanin Hengmei ya kasance kamfanin sayar da tufafi ga kasashen waje mafi girma ne a birnin Jiaxing, shugaban kamfanin Zhong Zhixin ya gaya mana cewa, ana amfani da sabbin fasahohin sadarwa kamar su bayanan kayayyaki kan intanet, da dimbin alkaluman da aka samu daga na'urorin sadarwa da komfuta, da na'urorin masu sarrafa kansu yayin da ake gudanar da sana'ar sakawa ta gargajiya, da haka ana iya rage lokacin da ake bukata, haka kuma ana iya tsimin kudin da aka kashe, yana mai cewa, "Hakika sauyin ya faru ne a cikin shekaru sama da goma kawai, lokacin da nake karami, na ga ana dinka tufafi ne cikin gida da keken da ake takawa da kafa, babu kamfanin samar da tufafi, daga baya an fara yin amfani da keken dinkin tufafi irin na lantarki, da keken dinki irin na masana'antu, yanzu haka ana amfani da na'urar kwanfuta domin samar da tufafi, nan gaba kamfaninmu zai kara maida hankali kan fasahohin zamani, ana saran cewa, kamfaninmu zai kasance kamfani na farko wanda ke samar da tufafi ta hanyar amfani da bayanan kayayyaki kan intanet da fasahar zamani ta 5G a fadin duniya." Zhong Zhixin ya kara da cewa, aikin samar da tufafi yana bukatar ma'aikata da yawa, misali jigilar kayayyaki ko dinka tufafi, nan gaba kamfaninsa na Hengmei zai kara maida hankali kan fasahohin zamani, ya ce: "Yanzu ma'aikatan kamfaninmu sun yi yawa, nan gaba zamu kyautata aikinmu, misali zamu kara yin amfani da na'urorin mutum mutumi wadanda zasu iya jigilar kayayyaki da ma'aikatan dake dinkin tufafi ke bukata a kusa da wurin aikinsu, kana zamu kara tantance dimbin alkaluman da aka samu daga na'urorin sadarwa da komfuta, domin tsai da kudurin samar da tufafi wadanda suka fi samun karbuwa daga wajen masu sayayya." Rukunin Jushi na kasar Sin yana samarwa da kuma sayar da kayayyakin gilas, kawo yanzu ya riga ya kafa sansanonin samar da kayayyakin gilas guda biyar a fadin duniya, wato birnin Tongxiang na lardin Zhejiang, da birnin Jiujiang na lardin Jiangxi, da birnin Chengdu na lardin Sichuan, da birnin Suez na kasar Masar, da jihar South Carolina ta kasar Amurka, kowace shekara, adadin kayayyakin gilas da rukunin ke samarwa ya kai tan miliyan 1 da dubu 600, ana sayar dasu zuwa ga wurare daban daban na kasashe da yankuna fiye da 100 a fadin duniya. Yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko da aka gudanar a birnin Shanghai a watan Nuwamban shekarar 2018, rukunin ya daddale wata kwangilar shigo da kayayyaki daga waje da yawanta ta kai dalar Amurka miliyan 100, ana sa ran rukunin zai samu ci gaba ta hanyar shigo da kayayyakin da yake bukata. Mataimakin shugaban kamfani na shida na rukunin Jushi na kasar Sin Gu Jianding ya bayyana cewa, har kullum rukunin Jushi yana samun ci gaba ta hanyar kyautata fasahar samar da kayayyakin gilas, ya ce: "Da farko, muna amfani da fasahohin sadarwa na zamani, misali muna amfani da dimbin alkaluman da aka samu daga na'urorin sadarwa da komfuta domin kyautata fasaharmu ta samar da kayayyakin gilas, kana muna kara amfani da na'urorin zamani, musamman ma wajen aikin jigilar kayayyaki masu nauyi, ta yadda zamu kyautata aikinmu yadda ya kamata." An ce, a halin da ake ciki yanzu, manyan kamfanonin da aka kafa a Wuzhen sun riga sun kai 93, a cikinsu, kamfanoni wadanda darajarsu ta kai kudin Sin yuan miliyan 100 sun kai 22, kana kamfanoni wadanda ke gudanar da harkokin dake da nasaba da tattalin arzikin zamani sun kai 484, ban da haka, daga watan Janairu zuwa watan Agusta na shekarar 2018, kwatankwacin adadin kudin da aka samu daga wajen masana'antu a garin ya kai yuan biliyan 6 da miliyan 190, haka kuma adadin jarin da aka zuba a garin ya kai yuan biliyan 2 da miliyan 820. Darektan kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na garin Wuzhen Jiang Wei ya bayyana cewa, garin Wuzhen yana jin dadin moriyar da ci gaba mai inganci yake kawo masa. Kan batun game da yadda garin zai kara bunkasa a nan gaba, Jiang Wei ya yi nuni da cewa, Wuzhen zai ci gaba da nacewa ga samun ci gaba mai inganci, wato zai yi kokarin kiyaye halayyar musamman tasa ta gari mai arzikin ruwa da al'adu, yana mai cewa, "Wuzhen zai nace ga manufar ci gaba ta yanzu, wato zai yi kokarin samun ci gaba mai inganci a fannonin yawon shakatawa da kiyaye muhalli da halittu masu rai da marasa rai, da raya sana'o'in dake da nasaba da intanet, ya zama dole gwamnatin garin ta fitar da manufar raya garin bisa tushen maida hankali kan moriyar al'ummar garin, kana garin yana sauke nauyin kasa bisa wuyansa, wato yana karbar bakuncin shirya babban taron intanet na kasashen duniya, wannan aiki ne da kasar Sin ta bashi, dole ya kammala aikin cikin nasara."

To, masu sauraro yau da wannan bayani muka kawo karshen shirinmu na yau na "Allah daya gari bamban" wanda ya yi bayani game da garin Wuzhen na birnin Tongxiang na lardin Zhejiang dake kudu maso gabashin kasar Sin. Ni ce Jamilah ke cewa, ku huta lafiya daga nan sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin na CRI, sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila)