logo

HAUSA

Hajiya Bintu Zarma(II)

2019-05-07 07:04:40 CRI

A cikin shirinmu na yau, za mu dora ne kan shirinmu da ya gabata, inda ku kasaurari hirar Abokiyar aikinmu Fa'iza Mustapha da Hajiya Bintu Zarma, mataimakiyar shugaba ta biyu ce ta kungiyar mata ta jihar Borno. Idan ba ku manta a kashin farko na hiran makon da ya gabata Hajiya Bintu ta bayyana ra'ayinta kan yadda kungiyar ta ke taimakawa mata a fannin karatu da aikin yi, har ma ta musunta kalaman da aka yi cewa, wai mata ba su iya shugabanci ba, su kan yi wasa da shugabanci. Amma a ganinta, ko da yake matan Najeriya sun tashi, sun fara ba da gudummawa ga ci gaban kasar, amma akwai sauran rina a kaba. Don haka ta yi kira ga mata da suka rike mutuncinsu a ko da yaushe. (Kande Gao)