Ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin a wasu kasashen Afirka a shekarar 2019
2019-05-07 08:59:46 CRI
Daga ranar 2 zuwa 6 ga watan Janairun shekarar 2019 ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ziyarci wasu kasashen nahiyar Afirka guda hudu. Wannan ziyara dai wata dadaddiyar al'ada ce ta tsawon shekaru 29 da kowane ministan harkokin wajen kasar Sin ke fara ziyartar kasashen Afirka a farkon kowace sabuwar shekara.
Wannan mataki ya kara nuna muhimmancin da kasar Sin ta dora kan alakarta da nahiyar Afirka, da ma kasashe masu tasowa. Haka kuma matakin ya kara jaddada kudurin kasar Sin na samun ci gaba tare gami da kyakkyawar makoma.
A yayin rangadin da ya kai shi kasashen nahiyar hudu, Wang kana mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, ya tattauna da shugabannin Afirka kan yadda za a aiwatar da matakan da aka tsara a taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da ya gudana cikin watan Satumban shekarar 2018 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Kasar Sin ta kara tabbatar da cewa, ita sahihiyar kawa ce kuma abokiyar hadin gwiwar nahiyar Afirka, bisa ga sahihan manufofi da irin sakamako na zahiri da imanin da take nunawa. Bugu da kari, kasar Sin tana mutunta zabin al'ummar Afirka na bin hanyar ci gaban da ta dace da yanayinsu, haka kuma ba ta taba tilasta musu yin wani abu ko gindaya musu wani sharadi ba. Kana idan suka fuskanci wani kalubale ko matsaloli, kasar Sin ta kan nemi hanyar ba su taimako ta hanyar da ta dace ta hanyar tattaunawa da abokan huldar ta Afirka. A shirye kasar Sin take ta taimakawa Afirka, a lokacin da bukatar hakan ta taso. Cikin gomman shekaru ke nan a jere, kasar Sin tana tura tawagogin ma'aikatan lafiya zuwa kasashen Afirka domin yakar cututtuka, baya ga masana aikin gona da samar da taimakon kudi da kwarewa da take bayarwa domin farfado da ababan more rayuwa da kawar da talauci.
A bana dai ministan harkokin wajen na kasar Sin Wang Yi ya ziyarci kasashen Habasha, da hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka da kasar Burkina-Faso da Gambia da kuma Senegal. Manufar wannan ziyara ita ce, sada zumunta, kuma dukkan sassan biyu suna goyon bayan juna da ma yin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban da kara raya shawarar "ziri daya da hanya daya", kana suna martaba manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.
Ana fatan shiryen-shiryen da kasar Sin ta gabatar za su bude wani sabon babi kan alakar dake tsakanin Sin da Afirka a cikin shekaru uku masu zuwa da nan gaba, a wani mataki na gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama. Saboda muhimmancin wannan dangantaka tsakanin bangarorin biyu, har ta kai ga kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, abin dake kara nuna karfafa wannan dangantaka mai tarin alheri ga sassan biyu.
Daga karshe masu fashin baki na cewa, muddin ana bukatar cin gajiyar wannan dangantaka yadda ya kamata, wajibi ne bangarori biyu su mutunta alkawuran da suka cimma, mutunta juna, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu a bangarorin gwamnatoci da al'ummomin sassan biyu. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)