logo

HAUSA

Kasar Sin ta haramta amfani da Fentanyl

2019-05-07 08:53:19 CRI

A kwanakin baya ne, ma'aikatar tsaron jama'a ta kasar Sin da hukumar kiwon lafiyar kasar da hukumar kula da ingancin magungunan sha ta kasar, suka fitar da wata sanarwa cewa, daga ranar 1 ga watan Mayun bana, za a shigar da Fentanyl a cikin jerin magungunan sha da aka haramta yin amfani da su yayin jinyar marasa lafiya, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin za ta sanya Fentanyl cikin jerin miyagun kwayoyi. A baya dai, kasar Sin ta shiga wani hali sakamakon matsalar miyagun kwayoyi, wannan ya sa kullum take mai da hankali matuka kan manufar yaki da miyagun kwayoyi, haka kuma ta samu sakamako mai gamsarwa wajen hana yaduwar Fentanyl a fadin kasar. Matakin da kasar Sin ta dauka, ya shaida wa kasashen duniya cewa, gwamnatin kasar tana yaki da miyagun kwayoyi yadda ya kamata, haka kuma tana taka muhimmiyar rawa kan aikin yaki da miyagun kwayoyi tare da sauran kasashen duniya.

Fentanyl dai magani ne da ke hana jin zafi, ya ninka Heroin karfi har sau 50, kana ya ninka Morphine sau 100. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, an fara tace sabon nau'in miyagun kwayoyi ta hanyar yin da amfani da Fentanyl a Amurka da Canada da sauran kasashen duniya, kuma adadin mutanen da suka mutu sakamakon shan Fentantl ya kai 18,335. Amma Amurka ba ta dauki matakin da ya dace na dakile matsalar ba, sai dai ta rika suka cewa, Fentanyl ya samo asali ne daga kasar Sin.

Kasar Sin ta dade tana gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da Amurka kan matakan yaki da Fentanyl, misali a taron musanyar bayanan yaki da miyagun kwayoyin da aka kira a watan Oktoban shekarar 2017, kasar Sin ta gabatar da bayanai sama da 400 game da yadda ake sayen Fentanyl ga bangaren Amurka.

Masu sharhi na ganin cewa, matakin da kasar Sin ta dauka, zai hana masu ta'ammali da miyagun kwayoyi yin amfani da Fentanyl, don haka ya zama wajibi, kasashen duniya su hada kai don yaki da miyagun kwayoyi a fadin duniya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)