Rakiya Zakari
2019-05-07 07:04:40 CRI
Shirin In ba ku ba gida na farin cikin gayyato wata bakuwa daga Kano, tarayyar Najeriya, wato Hajiya Rakiya Zakari, wata mace da ke dora matukar muhimmanci kan karatun yaranta.
A cikin hirar abokin aikinmu Ahmad Fagam da Hajiya Rakiya Zakari, ta bayyana yadda ta tura yaranta uku zuwa kasar Sin don karo ilminsu, da kuma dalilin da ya sa ta fi son kasar Sin wajen karo ilmin yaranta.