logo

HAUSA

Margaret Chan: Ina nuna girmamawa ga babban aikin kasar mahaifiyata na yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare

2019-05-07 07:04:40 CRI

Margaret Chan: Ina nuna girmamawa ga babban aikin kasar mahaifiyata na yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare

A yayin babban taro na murnar cika shekaru 40 da kasar Sin ta soma yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare a kwanan baya, an sanar da jerin sunaye 100 wadanda ke sahun gaba wajen yin kwaskwarima, ciki har da madam Margaret Chan, wadda ta inganta hadin kai a fannin kiwon lafiya game da shawarar "Ziri daya da hanya daya". Shekarar 1978 shekara ce ta farko da aka soma gudanar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, ita ce kuma shekara ta farko da Margaret Chan ta soma aiki a hukumar lafiya ta yankin Hong Kong bayan kammala karatu a makaranta. A tsakanin ranar 4 ga watan Janairu na shekarar 2007 zuwa ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2017, Margaret Chan ta rike mukamin shugabancin hukumar kiwon lafiya ta WHO ta MDD, hakan ta kasance Basiniya ta farko data dare kujerar aikin babbar daraktar hukumar WHO. A yayin da take waiwayon manyan sauye-sauyen da kasar mahaifarta ta Sin ta samu a cikin shekaru 40 da suka gabata, Margaret Chan ta nuna girmamawa kan wannan babban aikin na yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare.