logo

HAUSA

LFP ta Faransa za ta sauya lokutan wasu wasanni na Ligue 1 domin masu sha'awar kwallo na kasar Sin daga shekarar 2020

2019-05-07 07:04:44 CRI

Shugaban hukumar kwallon kafa ajin kungiyoyin kwararru ta kasar Faransa ko LFP a takaice Mr. Didier Quillot, ya ce hukumar sa na da nufin matsar da wasu wasanni da ake bugawa a gasar ajin kwararru ta Ligue 1, tun daga kakar wasa ta shekarar 2020 da 2021, zuwa karfe 1 na rana, domin masu sha'awar kwallon kafa Sinawa su samu zarafin kallo. Mr. Quillot ya ce za a sauya wasu wasanni na ko wace ranar Lahadi a kasar, ta yadda za su dace da lokacin da Sinawa za su iya kallon su a saukake, kamar da yadda aka yi gwajin hakan yayin wasannin da suka gudana a baya bayan nan tsakanin Lyon da Monaco, da wasan Nice da PSG. Mr. Quillot ya ce a ganin sa, idan har ana fatan bunkasa gasar wasannin ajin kwararru na Faransa a kasar Sin, abu na farko shi ne gabatar da wasan ga Sinawa, sa'an nan a yayata su a kafofin sada zumunta, a kuma fadada damammakin nuna su a kafofin Talabijin, da kulla alaka da masu yayata wasanni. Quillot ya kuma ce a bara, an buga wasa daya na gasar "French Super Cup" a birnin Shenzhen na kudancin kasar Sin, wanda hakan ya taimaka wajen yayata gasar, da ma kungiyoyin da suka buga wasan a kasar Sin mai tarin al'umma. A fannin kasuwanci kuma, jami'in ya ce akwai bukatar samar da labarai masu nagarta, wadanda za su dace da manufar yayata gasar Ligue 1. Ya ce ana bukatar samar da babban tsarin kasa da kasa, wanda zai rika fayyace halin da gasar ke ciki gwargwadon kwazon kungiyoyin dake buga ta. Game da kasancewar gasannin Premier League, da La Liga, a matsayin gasanni na farko a wasannin da manyan kungiyoyin kasashen turai ke bugawa kuwa, Mr. Quillot ya ce yana fatan mayar da Ligue 1 zama ta 3 nan da shekara 2022. Ya ce na san cewa a kasar Sin ba a san Ligue 1 kamar yadda aka san gasannin Premier League da La Liga ba. Amma hakan ya faru ne sakamakon wasu dalilai masu yawan gaske. Daya daga wadannan dalilai a cewar sa shi ne, yadda hukumomin kwallon kafar wasu gasannin na turai suka dade suna yayata wasannin su, musamman a kasar Sin, tun kusan shekaru 10 zuwa 15 da suka gabata, yayin da hukumar gasar Faransa ta fara aiwatar da wannan manufa shekaru 3 kacal da suka gabata, don haka dole ne a dauki lokaci kafin Ligue 1 ta cimma nasarar da ta sanya gaba. Abu na biyu kuwa shi ne, kwazon kungiyoyin kulaflikan dake buga gasar ajin kwararru ta Faransa, a cewar Quillot, kungiyar Paris Saint-Germain dake kan gaba a kasar, a bana ta gaza cimma nasarar lashe gasar zakarun turai. Ya kara da cewa, "dole sai kulaflikan mu sun kara kwazo". Kuma mu kara yayata bayanai game da su, da taurarin 'yan wasan mu, ta yadda za mu kara kyautata yayata gasar Ligue 1. Quillot ya ce a yanzu haka gasar Ligue 1 ta kama hanyar tarar da takwararta ta Italiya wato Serie A, a fannin karbuwa da kima a idanun duniya. Yace yana fatan za su kai ga tarar da Bundesliga ta Jamus, amma kuma hakan aiki ne da za a kwashe tsawon lokaci ana yi, inda ya kuma bayyana kasar Sin a matsayin wuri da suke fatan tallata wasannin su. Kaza lika a cewar sa, Ligue 1 na fitar da kwararru a fannin horaswa, da kula da 'yan wasa. Amma akwai bukatar kara kwazo wajen inganta hakan. Ya ce kari kan hakan doke Ligue 1 ya matsa kaimi a fannin cimma manyan nasarori a gasar zakarun turai. Ga misali kungiyar kwallon kafa ta PSG, ta yi rashin nasara a gasar ta ta zakarun turai a bana, bayan ta kai zagayen kulaflika 16, inda ta yi rashin nasara a hannun Manchester United. Duk da cewa a gida kungiyar ita ke kan gaba, amma Quillot ya ce ba za a zargi Ligue 1 da laifin rashin nasarar kungiyar ba a gasar ta zakarun turai. Ya ce PSG tana kan gaba a gida, to amma haka ma abun yake ga kulaflika irin su Juventus a Italiya, da Bayern Munich a Jamus, da Barcelona da Real Madrid a Sifaniya. Hakan na sauyawa ne kadai a Premier League, inda ko wace kakar wasanni ke zuwa da na ta salo, wato ba a iya sanin wace kungiya ce za ta lashe gasar, amma sauran gasanni na kasashe kusan ana iya sanin wadanda za su lashe su a duk shekara. Don haka dai tasirin da PSG ke da shi a gida, kusan daya yake da na sauran kungiyoyi a kasashe su. A ganin jami'in, rashin nasarar PSG a Champions League, ba shi da nasaba da tasirin su a gida. Sun dai yi rashin nasara ne kawai a hannun Manchester United a wasan su na Paris, saboda Neymar bai buga wasan ba, an kuma buga musu bugun daga kai sai mai tsaron gida a karshen wasan, wannan tamkar wani rashin sa'a ne ya same su. Game da wasannin gida na Ligue 1, Quillot ya ce, a ganin sa gasar na baiwa kungiyoyi damar nuna kwarewar su. Ya ce yana fatan ganin kungiyar da za ta samu nasarar daukar kofi a bana nan da karshen wasan Mayu mai zuwa. A ganin sa wasannin da aka buga sun zo da ba zata, ciki hadda yadda kungiyar Guingamp ta doke PSG, duk da cewa Guingamp din ba ta samu gurbin buga gasar zakarun turai ba, hakan kuwa a ganin sa ya faru ne sakamakon rashin karfin gwiwa da sa'a da kungiyar ta rasa. Amma duk da haka, jami'in na ganin kungiyoyin kasar Faransa na da matasan 'yan wasa irin su Kylian Mbappe, da Nicolas Pepe, dake taka masu leda a kakar bana. Hakan ne ma ya sa ake hasashen ganin irin wadannan 'yan wasa sun samu zarafin komawa manyan kulaflikan kasashen turai sakamakon irin rawa da suka taka a Faransa. Ya ce "kasar mu ce ta daya wajen fitar da kwararrun 'yan wasa, ba ko shakka a kan haka. Muna da makarantun horas wa irin su na daya a duniya, wadanda suka kware wajen gogarwa, da ilmantar da 'yan wasa". "Mun dauki kofi na duniya a gasar kasar Rasha cikin watan Yulin da ya gabata inda muka je da 'yan wasa matasa masu jini a jika,".

A ganin Mr. Quillot, Hanya daya mafi dacewa ta tabbatar da wannan matsayi na kwallon kafar kasar Faransa, ita ce ta kyautata tattalin arzikin kungiyoyin kasar, ciki hadda damar watsa bayanai, da sayar da tikitin wasanni, da hanyar tattara harajin su, da daukar nauyi, da kuma cinikayyar kungiyoyin. Ya ce ta haka kungiyoyin kwallon kafar kasar za su bunkasa ribar su ta kasuwanci, su kuma kara rike matsayin su na fitar da taurarin 'yan wasa.(Saminu Alhassan)