logo

HAUSA

Fina-finan kasar Sin sun wuce wasan Kungfu

2019-05-07 07:04:47 CRI




Fina-finan kasar Sin sun wuce wasan Kungfu

Jama'a, ko kuna sha'awar fina-finai? ko fina-finan kasar Sin suna burge ku? Ko akwai wani fim na kasar Sin da ya fi ba ku sha'awa? Mene ne ra'ayinku kan hadin gwiwar Sin da Nijeriya a fannin shirya fina-finai?

A kwanan nan abin da ya fi janyo hankalin al'umma a birnin Beijing bai wuce ga bikin nuna fina-finai na kasa da kasa karo na tara wanda aka kaddamar a Asabar da ta gabata a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

 

Fina-finan kasar Sin sun wuce wasan Kungfu

To, kamar yadda bahaushe kan ce, "waka a bakin mai ita ta fi dadi", mun samu damar tattauna tare da malam Yahaya Babs, wani shahararren mai shirya finafinai a Tarayyar Najeriya, a game da harkar fina-finai. Sai a biyo mu cikin shirin, don jin karin haske.