logo

HAUSA

Paulline Tallen

2019-05-07 07:04:40 CRI

Yau shirin In Ba Ku Ba Gida yana farin cikin gabatar muku da wata bakuwa mai suna Paulline Tallen. Mrs Paulline Tallen, tsohuwar Minista kuma tsohuwar mataimakiyar Gwamnan jihar Plateau, kana mataimakiyar Gwamna mace ta farko a arewacin Nijeriya, a yanzu kuma, shugabar hukumar yaki da cutar kanjamau ta Nijeriya wato NCAA.

Cikin hirar da ke tsakanin wakiyarmu Fa'iza Muhammad Mustapha da Mrs Paulline Tallen, suka tattauna game da shirin kasashen Afrika da na kasar Sin na kara kaimi wajen yaki da cutar kanjamau da kuma yanayin ci gaban mata a Nijeriya. (Kande)