Ni'ima Umar
2019-05-07 15:56:57 CRI
Masu sauraro, yau shirin In ba ku ba gida na farin cikin gabatar muku wata bakuwa daga jihar Sokoto ta tarayyar Najeriya, wato Hajiya Ni'ima, wadda take aiki a nan kasar Sin yanzu.
A cikin hirar abokiyar aikinmu Fa'iza Mustapha da Hajiya A'ishatu, ta bayyana yadda take aiki a nan birnin Beijing, a matsayinta na wata mai sanya murya ga wasannin kwaikwayo na talibijin na Sin, da ra'ayinta kan harkokin mata a Sin, da ma rawar da mata ke takawa yayin da ake kokarin neman ci gaban dan Adam.(Kande Gao)