logo

HAUSA

Shirin raya yankunan Guangdong-HongKong-Macao na kasar Sin

2019-05-07 08:59:46 CRI

A ranar Litinin 18 ga watan Fabrairu ne kasar Sin ta fitar da wani shirin raya yankuna Guangdong-Hong Kong-Macao ko kuma Greater Bay area a turance. Bisa shirin, nan da shekarar 2022, gwamnati na fatan gina yanki na musamman da zai kunshi tsarin birane na zamani da fasahohin kirkire-kirkire da babu kamarsu a duniya. Sauran abubuwan sun hada da tsarin masana'antu da yanayin muhalli mai inganci. Haka kuma,a karkashin shirin, akwai takarda ta musamman wanda ke yin jagora kan hadin gwiwa da ci gaban da ake samu a halin yanzu da ma nan gaba kan yankin na musamman, daga yanzu har zuwa shakarar 2022 na atsakaicin wa'adi daga bisani kuma an kara wa'adin shirin na dogon lokaci zuwa shekarar 2035. Takardar ta kuma bayyana cewa, nan da shekarar 2022, karfin yankin zai karu, sannan ya kamata a kara karfafawa tare da fadada hadin gwiwa tsakanin Guangdong, Hong Kong da Macao, aka kuma kara bunkasa matakan ci gaban yankin. Sannan bisa tsarin, nan da shekarar 2035, ya kamata tsarin tattalin arziki da dabarun ci gaban yankin ya samu tallafin goyon bayan kirkire-kirkire, ta yadda karfinsa na tattalin arziki da fasahar kere-kere zata kara bunkasa, kana gasarsa a bangaren kasa da kasa da ma tasirinsa su kara yin karfi Shirin raya yankin Guangdong da Hong Kong da Macao, ko kuma Greater Bay Area a Turance, ya zama wurin da aka fi samun kwararar kwararru, yayin da kuma yake da damar jan hankalin kwararru na kasashen waje. A cewar wani rahoton hadin gwiwa da Jami'ar Tsinghua na kasar Sin da kamfanin LinkedIn China suka fitar, kan kwararru 439,000 da wasu 118,000 dake aiki a bangaren fasahar sadarwa a yankin, Yankin na daya daga cikin wuraren da suka fi jan hankali kwararru kan fasahar zamani a kasar Sin, domin ya zarce Beijing da Wuhan a wannan bangare. (Ahmad/Ibrahim/Sanusi)