logo

HAUSA

Malama Rekhan Guli: "Ba da hidima ga jama'a, da sanya iyaye na su yi alfarma domin aiki na, su ne alheri da nake ji."

2019-05-07 07:04:40 CRI

Tun daga shekarar 2000, aka soma gina azuzuwa na musamman don daukar daliban jihar Xinjiang a makarantun sakandare masu inganci kusan dari daya a birane sama da goma dake babban yankin kasar Sin, wadanda suka ci gaba a fannin ba da ilmi a nan kasar. Ya zuwa yanzu, an dauki daliban da suka fito daga kabilu daban daban na jihar Xinjiang da suka kammala karatu a makarantun midil da yawansu ya wuce dubu 90, inda kuma dubu 30 suka kammala karatu a jami'a, yawancinsu kuma sun zabi komawa jihar Xinjiang don su yi aiki, wannan wani sabon mataki ne na raya jihar. A cikin shirinmu na yau kuma, za mu yi muku bayani ne game da wannan tsari.