Matakan kasar Sin na raya tattalin arziki a shekarar 2019
2019-05-07 08:59:46 CRI
Kwararru da masana tattalin arziki sun yi hasashen yiwuwar ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2019, a yayin da mahukuntan kasar ke ci gaba da daukar kwararan matakan bullo da tsare tsaren da za su daga matsayin ci gaban tattalin arzikin kasar. Haka kuma, tattalin arzikin kasar zai daidaita ne bayan watanni uku na farko na shekarar 2019 kana ana sa ran zai daga sama a rubu'i na biyu na tsakiyar shekarar 2019. Ma'aunin tattalin arzikin (GDP) na kasar Sin ya karu da kashi 6.7 bisa 100 a farkon watanni ukun farkon shekarar 2018, idan an kwatanta da makamancin lokacin bara, har ma ya dara hasashen da gwamnatin kasar ta yi na samun karuwar tattalin arzikin kasar da kashi 6.5 bisa 100. Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki, da su dage wajen aiwatar da matakan daidaita ci gaban tattalin arziki, bisa matsakaicin matsayi,tare da kiyaye ka'idojin da aka tsara, da kaucewa matsin lambar kasuwanni, da cin gajiya daga alfanun sauye sauye, da bude kofa ga kasashen duniya. A shekarar bana, za a ci gaba da karfafa ayyukan zuba jari a kasar Sin, da kuma mai da hankali kan zuba jari bisa bukatun al'umma. A bana, za a karfafa ayyukan gina ababen more rayuwa a sabbin fannoni, wadanda suka hada da fasahar kwaikwayar tunanin bil Adama, da yanar gizo ta masana'antu, da kuma fasahar intanet ta 5G mai amfanawa harkokin kasuwanci. A sa'i daya kuma, za a karfafa ayyukan gina ababen more rayuwa a birane da karkara, da ayyukan sufurin kayayyaki, da kawar da talauci, da kuma raya makamashi da dai sauransu. A fannin zuba jari,gwamnatin Sin za ta ware kudade masu yawa ga ayyukan kaurar da matalauta, da samar musu gidaje, da aikin raya kauyuka, da gina manyan kayayyakin more rayuwa, da sabunta fasahohi, da kuma daidaita tsare-tsaren tattalin arziki. Haka kuma a bana gwamnati za ta kara zuba kudi bisa kasafin kudin da aka tsara, da kara saurin samar da kudaden ga fannonin dake da bukata, sa'an nan za a kara janyo hankalin 'yan kasuwa domin su ma su zuba karin kudi ga wasu manyan ayyukan gwamnati
Haka kuma, a bana, za a kawar da wasu manufofin dake hana shigowar jarin waje da gyara jerin fannonin da 'yan kasuwar ketare za su zuba jari a kasar Sin da jerin fannoni masu dacewa ta yadda 'yan kasuwar ketare za su zuba jari a yankunan tsakiya da yammacin kasar Sin, domin shigar da karin jarin waje a fannoni daban daban. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)