logo

HAUSA

Taron kolin AU na shekarar 2019

2019-05-07 08:59:46 CRI

A ranar Lahadi 10 ga watan Fabrairun shekarar 2019 ne, aka bude taron kolin kungiyar tarayyar Afrika (AU) karo na 32 a hedkwatar kungiyar dake Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha

Taken taron na kwanaki biyu na wannan shekara shi ne, "Sake dawo da 'yan gudun hijira gidajensu, da mutanen dake rayuwa a sansanonin tsugunar da wadanda rikici ya raba da gidajensu, inda ake fatan samo hanya mai dorewa don magance yadda ake raba jama'a da gidajensu a Afrika.

Batun tilastawa mutane barin gidajensu da 'yan gudun hijira a Afrika da kuma yiwa kungiyar AU gyaran fuska, da batun zaman lafiya da tsaro suna daga cikin muhimman batutuwan da suka mamaye taron kolin AU na bana. A jawabinsa na bude taron, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat, ya bukaci a kara kokari don dorawa kan irin nasarorin da aka cimma a bangarori daban daban, ciki har da batun kafa yankin ciniki cikin 'yanci a nahiyar, yiwa hukumomin kudi na kungiyar gyaran fuska.

A taron kungiyar na bana ne kuma, shugaba al-Sisi na kasar Masar ya karbi jagorancin karba-karba na kungiyar daga hannun shugaba Paul Kagame na Rwanda wanda ya kammala wa'adinsa na shekara guda.

Sabon shugaban kungiyar al-Sisi, ya bayyana kudurinsa na kara zage damtse wajen ganin an inganta rayuwar al'ummomin nahiyar yayin wa'adinsa na shekara guda. Shi ma shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aikewa kungiyar da sakon fatan alheri da taya murnar gudanar da taron kolin nata.

Sauran batutuwan da taron na bana ya tabo sun hada da ayyuka da shirye-shiryen da aka tsara aiwatarwa a nahiyar da yaki da ayyukan ta'addanci a yankin Sahel da tafkin Chadi da ma sauran kalubale dake addabar nahiyar Afirka. (Ahmed, Ibrahim /Sanusi Chen)