Hira da Ministar Kudi ta Tarayyar Najeriya Zainab Ahmed
2019-05-07 13:56:24 CRI
Masu sauraro, yau shirin In ba ku ba gida na farin cikin gabatar muku wata muhimmiyar bakuwa daga tarayyar Najeriya, wato Hajiya Zainab Ahmed, ministar kudi ta Tarayyar Najeriya, wadda ta zo kasar Sin don halartar taron koli na dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu. Bayan da ta halarci bikin bude taron, wakiliyarmu Fa'iza Mustapha ta samu damar yin hira da ita.
A cikin hirarsu, ministar ta ambaci makasudin zuwansu nan kasar Sin, da alfanun da Najeriya za ta samu idan ta sa hannu cikin shawarar "ziri daya da hanya daya", kana ta musunta zargin da ake cewa kasar Sin na dana wa Najeriya tarkon bashi. Bugu da kari kuma, a matsayinta ta mace, a cikin wannan shirin namu na "In ba ku ba gida", Hajiya Zainab Ahmed ta tabo maganar ci gaban mata da Najeriya ta samu, kana da kalubalen da take fuskanta a wannan fannin. (Kande Gao)