Madline Kullab: mai kamun kifi dake fama da mawuyacin halin da take ciki na zaman rayuwa a zirin Gaza
2019-05-07 07:04:40 CRI
A zirin Gaza dake gabashin bakin bahar Rum, akwai wasu mutane kusan dubu biyar suna aikin kama kifi domin zaman rayuwarsu, Madline Kullab, tana daya daga cikinsu. Tun da take shekarun haihuwa shida sai ta soma aikin kama kifi tare da mahaifinta, yanzu kuma ta kasance mai kama kifi mace ta farko, kuma daya kacal a zirin Gaza. Kwanan baya, wakiliyarmu ta samu damar kai mata ziyara, a cikin shirinmu na yau za mu yi muku bayani ne game da labarin ta.