logo

HAUSA

Bikin Ranar Rediyo ta Duniya ta shekarar 2019

2019-05-07 08:59:46 CRI

A ranar 13 ga watan Fabrairu na kowace shekara, rana ce ta bikin ranar rediyo ta duniya, wadda MDD ta ayyana a matsayin ranar Rediyo ta duniya tun a shekara ta 2011. Ranar Radio ta Duniya, rana ce da aka kebe don duba tasirin da radiyo ke da shi wajen inganta rayuwar jama'a. A ko da yaushe, gidajen rediyo wurare ne dake bayar da dama ga jama'a domin sanar da su irin wainar da ake toyawa a duniya ta kowane fanni na rayuwar dan Adam, tashoshin rediyo suna kokari matuka wajen samar da labaru da dumi-duminsu, wadanda ke tsage gaskiya komi dacinta tare da sanar da mai sauraro irin abubuwan dake faruwa a kasashen duniya baki daya.

A shekara ta 2011 ne hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ilmi, kimiyya, da al'adu, watau UNESCO, ta kebe kowace ranar 13 ga wata Fabarairu a matsayin ranar Radiyo ta Duniya. Taken bikin ranar radio ta wannan shekarar ta 2019 shi ne "Tattaunawa, hakuri da juna da zaman lafiya". Rediyo wata muhimmiyar kafar isar da sakonni ne wanda ta shahara a duk fadin duniya musamman wajen irin rawar ta take takawa na ilmantar da alumma, wayar da kan jama'a, nishadantarwa, wannan kuwa ya shafi dukkan yankuna na duniya kama daga birane har ma yankunan karkara. A cewar hukumar ta UNESCO, rediyo na kan gaba a matsayin hanyar sadarwa ga al'umma mai yawa a ko'ina a duniya, a kuma cikin lokaci kankani. (Ahmad Fagam, Ibrahim Yaya)