logo

HAUSA

Shugabannin kasar Cape Verde sun gana da ministan wajen kasar Sin

2017-05-21 16:43:43 CRI

Shugaban kasar Cape Verde Jorge Carlos Fonseca da firaministan kasar Ulisses Correia e Silv sun gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi daya bayan daya a birnin Praia, fadar mulkin kasar, a jiya Asabar.

A cewar shugabannin kasar Cape Verde, kasar Sin babbar aminiya ce ta kasarsu, wadda ta taimakawa Cape Verde sosai bayan da kasar ta samu 'yancin kanta. A wannan zamanin da ake ciki, kasar Cape Verde tana marawa kasar Sin baya kan shawararta ta "ziri daya hanya daya", inda take son yin amfani da wannan dama don zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen 2, da sanya kasar Cape Verde ta zama abokiyar dake kokarin hadin kai tare da kasar Sin ta fuskar manyan tsare-tsare, tare da zamantowa abokiyar kasar Sin mafi kusanci a nahiyar Afirka.

A nasa bangaren, firaministan kasar Sin Wang Yi ya ce, kasar Sin na son aiwatar da ayyukan hadin kai bisa ra'ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma a baya, da zurfafa huldar hadin gwiwa tare da kasar a fannonin sarrafa albarkatun teku, da raya yankin musamman na tattalin arziki, da yawon shakatawa, da gina kayayyakin more rayuwar jama'a, da makamantansu. Ta wannan hanya, kasar Sin na neman taimakawa kasar Cape Verde, don ta yi amfani da albarkatunta wajen neman samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa.(Bello Wang)