logo

HAUSA

Ministan wajen kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Cape Verde

2017-05-21 16:43:43 CRI

Duk a birnin Praia na kasar Cape Verde, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Cape Verde, Luís Filipe Tavares, a jiya Asabar.

Yayin ganawar tsakanin manyan jami'an 2, Mista Wang Yi ya ce, shawarar "ziri daya hanya daya" da kasar Sin ta gabatar ta shafi kasar Cape Verde. Bisa yin la'akari da tarihi, kasar Cape Verde na kusa da hanyar siliki ta teku, wadda ta taka rawar gani a fannin cinikayyar da aka yi tsakanin kasar Sin, da sauran kasashen dake nahiyar Asiya da Afirka. Saboda haka, kasar Sin na fatan ganin Cape Verde za ta kara taka muhimmiyar rawa a kokarin halartar shawarar "ziri daya hanya daya". A cewar ministan kasar Sin, kasar tana yiwa kasar Cape Verde godiya kan goyon bayan da ta nunawa kasar Sin kan kokarinta na kare moriyar kanta, da kula da wasu batutuwan da ke jan hankalinta. Sa'an nan a nata bangaren, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin kare hakkin kasar Cape Verde, da na sauran kasashe masu tasowa.

A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Cape Verde, Luís Filipe Tavares, ya ce kasarsa na son zama aminiyar kasar Sin, wadda take hadin gwiwa da ita a wasu manyan tsare-tsare, musamman a fannin sarrafa albarkatun teku.(Bello Wang)