Ranar 19 ga watan Afrilun shekarar 2016, shugaba Xi Jinping ya shugabanci taron bita kan tsaron yanar gizo ta Intanet da harkokin sadarwa, tare da yin muhimmin jawabi, inda ya mai da hankali kan yadda ake tafiyar da harkokin Intanet, muhimmiyar fasaha da sauran manyan batutuwa, ya kuma tsara manufar kasar dangane da raya kasar Sin mai karfin Intanet da kara azama kan bunkasar ayyukan Intanet da sadarwa.
A cikin shekaru 3 da suka shude, kasar Sin ta dauki matakai da dama:
1. Kasar Sin ta fito da kundin tsare-tsaren raya harkokin sadarwa na kasar, inda aka tsara babban shirin kasa na raya harkar sadarwa nan da shekaru 10 masu zuwa.
2. Kasar Sin ta fito da manyan tsare-tsare kan tabbatar da tsaron Intanet, a kokarin kiyaye 'yanci, da tsaron kasa da ma muradunta a fannin Intanet.
3. Kasar Sin ta fito da dokar tabbatar da tsaron Intanet, wadda muhimmiyar doka ce ta farko a kasar Sin ta fuskar tabbatar da tsaron Intanet.
4. Kasar Sin ta fito da kundin tsarin dokokin al'umma, inda aka tabbatar da ba da kariya kan bayanan al'umma, dukiyoyinsu da ba na gaskiya ba.
A cikin wadannan shekaru 3 da suka wuce, kasar Sin ta fito da wasu manyan tsare-tsare da manufofi daya bayan daya don kara bunkasa harkokin sadarwa. Kasar Sin ta kara samun tabbaci ta fuskar manufa yayin da take kokarin zama kasa mai karfin Intanet. (Tasallah Yuan)