A yayin tattaunawar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, batun muhimmiyar alama ce a tarihin zamanin da da na yanzu. A cewarsa, a yayin da ake tunawa da ranar, dole ne a kara nazarinta da jagorantar matasan kasar Sin da su yi kokari bisa tunanin abun da ya faru, don kafa zaman al'umma mai matsakaicin karfi, da raya tsarin gurguzu da ke da halin musamman na kasar Sin, da kuma cimma burin farfado da al'ummar kasar Sin.
A ranar 4 ga watan Mayun shekarar 1919 a nan birnin Beijing, aka tayar da wata zanga-zangar kishin kasa, wadda ke adawa da mulkin mallaka da wasu manyan kasashen duniya masu fada a ji suka gudana a nan kasar Sin, da tsarin mulkin kama karya, inda dalibai matasa na jami'o'i tare kuma da wasu fararen hula, da mazauna birnin da 'yan kasuwa da masu tafiyar da masana'antu suka halarta tare. (Bilkisu)