Hakan ya biyo bayan fitar da wani daftari da hukumar tsara kudurorin samar da ci gaba, da aiwatar da gyare-gyare ta Sin ko NDRC, tare da ma'aikatar cinikayya ta kasar suka yi, bisa wasu takardun bayanai biyu da aka yiwa gyara. Daya game da jawo jarin waje zuwa dukkanin sassan kasar, yayin da dayan kuma ya shafi jarin da ake fatan jawowa zuwa yankuna masu karancin ci gaba, dake tsakiya da yammacin kasar, da ma tsohon yankin masana'antu na arewa maso gabashin kasar, da kuma yankunan lardin Hunan dake kudu mai nisa ta kasar.
Hukumar NDRC ta ce burin daukar wannan mataki dai shi ne sanya karin masana'antu cikin jerin da ake da shi, da kyautata tsarin aiwatar da manufofin bunkasa masana'antu, da tabbatar da ci gaban masana'antun dake dogaro da jarin waje cikin kyakkyawan yanayi. (Saminu Hassan)