Sabon binciken ya nuna cewa, kaso 61 cikin 100 na manyan masana harkar mai da iskar gas a kasar ta Sin sun bayyana cewa, kungiyoyinsu sun dukufa wajen karkata ga amfani da makamashin da ba ya fitar da abubuwan dake gurbata muhalli, idan aka kwatanta da kaso 51 cikin 100 dake da wannan ra'ayi a duniya baki daya.
Bugu da kari, nan da shekarar 2020 shugabannin kamfanonin kasar Sin za su kara mayar da hankali wajen rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da a kalla kaso 15 cikin 100 cikin matakan da aka tsara a shekarar 2015.
Rahoton hukumar ya kuma nuna cewa, wasu karin rukunin kamfanonin mai da iskar gas a sassan kasar Sin na kokarin ganin sun aiwatar da manufar gwamnati game da kiyaye gurbatar mahalli. (Ibrahim)