A yau Alhamis da safe, Mr. Liu He, mamban hukumar siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firaministan gwamnatin kasar, sannan jagoran bangaren Sin kan tattaunawa game da batun tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka daga dukkan fannoni, da Mr. Robert Lighthizer, wakilin cinikayya na Amurka da Steven Mnuchin, ministan kudin Amurka su uku sun shugabanci bikin kaddamar da taron tattaunawa kan batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka daga dukkan fannoni a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin.
Bisa ajandar da aka kafa, za a yi wannan zagayen tattaunawa ne tsakanin ranar 14 da 15 ga wannan watan na Fabrairu. (Sanusi Chen)