Rahoton mai taken "Yadda ake kallon kamfanonin kasar Sin a duniya" wanda kamfanin ba da shawarwari mai suna Brunswick ya wallafa, ya tattara bayanansa ne kan binciken da ya gudanar a kasashe 18 da kamfanonin kasar Sin suke da jari da ma shirye-shirye, da kuma hirarraki da ya gudanar da manyan shugabannin kamfanonin kasar Sin 300 dake gudanar da ayyukansu a kasashen ketare ko kuma suke da shirin yin haka.
Kamfani ya gudanar da wannan bincike ne daga watan Oktoba zuwa Nuwamban da ya gabata a kasashe da suka hada da Amurka da Burtaniya da Jamus da Singapore. Sauran sun hada da Malaysia da Indonesia da Najeriya da Kenya da Kazakhstan da kuma Hungary.
A cewar rahoton, shugabannin 'yan kasuwan kasar Sin na ganin cewa, yadda kamfanonin kasar suka fadada harkokinsu zuwa kasashen ketare, shi ne kashin bayan dorewar ci gabansu.
Haka kuma a yayin da suke amfani da damar kara sayar da hajojinsu a kasuwannin cikin gida, kamfanonin na kara zakulo karin damammaki, inda rahotanni ke cewa, a shekarar da ta gabata kaso 49 cikin 100 na kayayyakin da kasar ke fitarwa da wadanda take sayarwa sun kasance masu matukar muhimmanci. (Ibrahim Yaya)