Ma'aunin tattalin arzikin kasar na (GDP), zai iya kaiwa kusan dalar Amurka trillion 13, in ji Ning Jizhe, mataimakin shugaban hukumar bunkasa ci gaba da yin sauye sauye na kasar Sin, wanda ya bayyana hakan a lokacin wani taron dandali.
A 'yan shekarun da suka gabata, matsakaicin karuwar kudaden shigar al'ummar kasar ya kusa kaiwa miliyan 400, yayin da a wannan shekarar adadin ya zarta miliyan 400, wanda hakan ya kafa wani muhimmin tushe na kawo sauyi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar, inji Ning.
A wannan shekarar, kasar Sin za ta bayar da gudunmowar kashi 30 bisa 100 na saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya, kana ma'aunin GDPn kasar Sin zai bayar da gudunmowar kashi 16 bisa 100 na bunkasuwar GDP na duniya baki daya, in ji Han Wenxiu, wani jami'in hukumar al'amurran kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiya. (Ahmad Fagam)