Wadannan kasashe a cewar rahoton mai take, "Zaburar da duniya da harkokin kirkire-kirkire" sun hada da Afirka ta kudu da Kenya da Mauritius da kuma Rwanda. Inda ya nuna cewa, cin gajiyar kimiya da fasahar kere-kere, da ilimi mai zurfi da kwararrun ma'aikata sun karfafawa tattalin arzikin kasashen na Afirka gwiwar yin takara.
Alkaluman rahoton sun nuna cewa, tun daga shekarar 2012 kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar Sahara ne, suke cikin kungiyoyin da suka yi nasara a wannan fanni.
A halin da ake ciki kuma wani rahoto da kugiyar kare 'yan cin mallakar fasaha ta duniya (WIPO) da abokan hulda daga jami'o'I da sauran masu ruwa da tsaki a wannan harka suka wallafa, sun nuna cewa, yana da muhimmanci kasashen na Afirka su rike matsayin da suke a wannan fanni .(Ibrahim)