Geng Shuang ya yi wannan bayyani ne, biyo bayan wasu rahotannin da aka bayar cewa, bangaren kasar Amurka ya bayyana a kwanakin baya cewa, yawan hasarar da kasar Amurka ta yi a sakamakon rikicin ciniki a tsakaninta da kasar Sin bai kai hasarar da kasar Sin ta yi ba, kasar Sin ta fi fuskantar matsin lamba kan wannan batu. Tattalin arzikin Sin ba shi da kyau a yanzu, kana rikicin ya kawo illa sosai ga harkokin ciniki da zuba jari a kasar.
Game da wannan batu, Geng Shuang yana fatan kasar Amurka za ta saurari kiran da bangaren sana'o'i da masu sayayya na kasar Amurka suka yi, kana ya yi la'akari da ra'ayin kasashen duniya na tsayawa tsayin daka kan ra'ayin kasancewar bangarori daban daban da yin ciniki cikin 'yanci. Ya kamata kasar Amurka ta gaggauta dakatar da ra'ayin bangare daya da bada kariya ga harkokin cinikayya. (Zainab)