An ba da labarin cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin da asusun Song Qinglin na Sin da gwamnatin lardin Sichuan ne suka hadin kai don gabatar da bikin a wannan karo, wanda za a kwashe kwanaki 8 wajen gudanar da shi, inda matasan za su ziyarci Beijing da Chengdu, domin ganewa idonsu yankunan ayyukan kimmiya da fasaha da shahararrun wurare yawon shakatawa, tare kuma da kai ziyara wasu hukumomin gwamnati, ungwani, da jami'o'i don tuntubar matasan wuraren.
Shugaban sashin Afrika na ma'aikatar harkokin waje Msita Dai Jun ya yi bayanin cewa, ana gudanar da irin wannan biki ne don tabbatar da sakamakon da aka samu cikin taron koli da aka yi a Johannesberg a shekarar 2015 na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika. Mahalartan matasa ne 'yan Afrika 1000 da suka fito daga kasashen Afrika 54 dake cikin tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika, ciki hadda Burkina Faso wadda ba ta dade da shiga dandalin ba, al'amarin da ya sa bikin a wannan karo ya fi girma da samun mahalarta mafi yawa. (Amina Xu)