Amma, abin bakin ciki shi ne, bangaren Amurka ya yi kunnen uwar shegu da ra'ayin bai daya da bangarorin biyu suka cimma, kana ya tayar da yakin cinikayya. Matakin da Amurka ta dauka, ba kawai ya lahanta moriyar bangarorin biyu ba ne, har ma ya gurgunta tsarin cinikayyar duniya, don haka bangaren Sin ya nuna rashin amincewarta da hakan.
Kakakin ya ce, kasar Sin bata fatan yakin ciniki. Amma a sabili da mataki maras moriya da bangaren Amurka ya dauka, kasar Sin ba yadda za ta yi, illa ta dauki kwararan matakai na mayar da martani, ta yadda za ta iya kare moriyar kasar da ta jama'arta, da kare tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda, da wani tsarin kasuwanci da ya shafi bangarori daban daban.
Kaza lika kasar Sin za ta dauki matakin karbar haraji da ya yi daidai da wanda kasar Amurka ta dauka. Kana sakamakon da bangarorin biyu suka samu a kwanakin baya wajen shawarwarin da suka gudanar ya zama maras amfani ke nan.
Kakakin na kasar Sin ya kara da cewa, a zamanin da muke ciki, ta da yakin ciniki bai dace da moriyar duniyar mu ba. Saboda haka, kasar Sin ta yi kira ga kasashe daban daban, da su dauki mataki na bai daya, don nuna kin amincewa da duk wani mataki na maida hannun agogo baya, game da burin kare babbar moriyar bil Adama.