Mataimakin ministan ciniki na kasar Sin zai tafi Amurka don halartar shawarwari kan batun tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka
Bisa labarin da ma'aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin ta bayar a ranar 16 ga wata, an ce, mataimakin ministan ciniki na kasar Sin, kuma mataimakin wakilin shawarwari kan cinikin dake tsakanin kasa da kasa Wang Shouwen, zai jagoranci wata tawaga da za ta kai ziyara kasar Amurka a karshen watan Agusta, inda zai yi shawarwari tare da tawagar kasar Amurka, karkashin jagorancin mataimakin ministan kudi na kasar Mr. Malpasse, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka.
Sin ta jaddada cewa, ba ta amince da ra'ayin bangare daya ba, da ba da kariya ga cinikayya, da kuma matakan kayyade ciniki daga bangare daya. Kaza lika Sin ta yi maraba da yin shawarwari, da mu'amala bisa tushen adalci da daidaito, da kuma yin imani da juna. (Zainab)