Bisa amincewar majalisar gudanawar kasar Sin, hukumar kula da haraji ta majalisar, ta yanke shawarar sanya karin haraji na kaso 25 kan kayayyaki 659 da Amurka ke shigarwa Sin, wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 50.
A cewar hukumar kula da harkokin harajin, karin haraji kan kayayyaki 545 da darajarsu ta kai dala biliyan 34, ciki har da kayakin gona da ababen hawa da kayan ruwa, zai fara aiki ne daga ranar 6 ga watan Yuli mai kamawa.
Ta kara da cewa, za a sanar da ranar da za a fara amfani da karin harajin kan kayayyaki 114 da suka hada da sinadarai da kayakin kiwon lafiya da na makamashi, a nan gaba kadan.
Wani jami'in hukumar ya ce, fara aiwatar da harajin da aka kakabawa kayakin kasar Sin, zai sauya sharudan cinikayyar kayayyakin, sannan zai shafi masu samar da su da kamfanonin cinikayya da kuma masana'antun dake da ruwa da tsaki wajen samar da kayyakin.
Jami'in ya ce kasar Sin ta dauki matakin ne domin mayar da martani ga abubuwan da Amurka ta yi, wadanda suka sabawa dokokin kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)