Sin ta ki amincewa da matakin Amurka na shigar da wasu kamfanoninta cikin jerin kamfanonin da Amurkar ta hana fitar musu da kayyayaki
Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, ya bayyana cewa, kasarsa ba za ta amincewa matakan da Amurka ta dauka daga bangare guda kan kamfanoninta ba. Kakakin ya bayyana haka ne a jiya, dangane da matakin Amurka na shigar da wasu kamfanonin Sin cikin jerin sunayen kamfanonin da ta hana fitar musu da kayyayaki.
Jami'in ya ce, kasar Sin ta kalubalanci Amurka, da ta dauki matakan da suka dace, da sassauta manufofin fitar da kayyyaki zuwa kasar Sin, da tabbatar da sa kaimi ga ciniki da hadin gwiwar dake tsakanin kamfanonin kasashen Sin da Amurka a fannin fasahohin zamani, da kuma tabbatar da moriyar kamfanonin kasashen biyu yadda ya kamata. (Zainab)