Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a jiya cewa, Sin na nuna rashin jin dadi matuka kan wasu ayoyi dake da nasaba da kasar Sin da Amurka ta rubuta a daftarin dokar tsaron kasarta na shekarar 2019, inda ta kalubalanci Amurkar da ta soke wadannan abubuwa.
Geng Shuang ya ce, idan har ta zartas da wadannan abubuwa, matakin zai iya kawo illa ga aminci dake tsakanin Sin da Amurka, da ma yadda hakan ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da hadin kan kasashen biyu a tekun Taiwan. Haka kuma kasar Sin na kalubalantar Amurka da ta yi watsi da tunanin yakin cacar baki, ta kuma soke wadannan abubuwa a cikin dokarta, ta yadda za a raya dangantaka mai dorewa tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. (Amina Xu)