A hakika dai, zargin da Amurka ta yi wa kasar Sin ba shi da tushe, kana ya saba da gyare-gyaren da kasar Sin ta yi kan tsarin farashin musayar kudin RMB. Kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya ce, farashin musayar kudin Sin na canjawa ne bisa yanayin kasuwanni, kuma, Sin ba ta son fitar da karin hajoji zuwa ketare ta hanyar rage farashin musayar kudin RMB. (Maryam)