Shugaban jihar Colorado John Hickenlooper ya nuna cewa, zurfafa hadin kan Sin da Amurka zai bada gudunmawa ga raya dangantakar kasashen biyu yayin da suke fuskantar takaddama da mawuyancin hali a tsakaninsu. Jihar za ta ci gaba da kara hadin kai da kasar Sin da kara fahimtar juna da amincewa da juna.
Shugaban jihar Utah, Gary Herbert, shi ma ya bayyana a gun taron cewa, Amurka na bukatar shiga kasuwannin duniya, ya kamata kasar ta kara hadin kai da tuntubar juna da kasashen duniya a maimakon rufe kofarta.
Ban da wannan kuma, shugabannin jihohi daban-daban mahalartan taron sun bayyana ra'ayinsu na kara hadin kai da kasar Sin, a ganinsu takaddamar da Amurka ta tayar a fannin ciniki ta kawo illa ga kayayyakin gona da sauran kayyaki masu kyau da Amurka take fitarwa kasashen waje, har ma ta samar da rashin tabbas a fannin zuba jari da bunkasuwar wasu kamfanonin kasar. (Amina Xu)