An kammala taron ministocin kudi da shugabannin manyan bankuna na kasashen G20 na yini biyu a Buenos Aires hedkwatar Argentina. Batun ciniki shi ne ya fi jawo hankalin mahalarta taron. Ko da yake, taron ya ba da wata hadaddiyar sanarwa don nanata wajibcin tinkarar hadarin da takaddamar ciniki ke jawo wa tattalin arzikin duniya, amma ministan kudin kasar Faransa Bruno Le Maire ya nuna cewa, ya kamata Amurka ta kawar da harajin da ta sanya kan karafa da sanholo, idan ba haka ba, EU ba za ta yi shawarwari da Amurka kan ciniki cikin 'yanci ba.
Sin, EU, Canada, Mexico, Indiya da Turkiya da sauransu sun dauki matakin da ya dace don mai da martani ga matakin tsokana da Amurka ke dauka babu dakata, kuma sun gabatar da korafi a gaban WTO. Dukkanin matakan da kasashe daban-daban ke dauka na da zummar yin shawarwari bisa tsarin WTO. (Amina Xu)