Peng Liyuan ta ce, yara su ne makomar kasa, muna fatan za a sada kyakkyawan zumunci a tsakanin yaran Sin da na Afirka ta Kudu, ta yadda za a ciyar da daddaden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu gaba.
A safiyar wannan rana kuma, Peng Liyuan ta halarci bikin kammala horaswa da aka shirya ga malaman yara a birnin Pretoria. (Maryam)