Shugabannin Sin da Afrika ta kudu sun cimma matsaya daya kan raya dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni

A jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa a Pretoria, hedkwatar kasar. Yayin ganawar tasu, shugabannin biyu sun jinjinawa zumunci dake tsakanin kasashen biyu, tare da cimma matsaya kan raya dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a sabon karni, da kara tuntuba tsakanin manyan jami'an bangarori daban, da zurfafa amince da juna a fannin siyasa, da yin musanyar ra'ayi kan raya kasa, da sa kaimi ga hadin kai, da zurfafa mu'ammalar al'adu, ta yadda jama'ar kasashen biyu za su amfana. (Amina Xu)